Wednesday, May 13
Shadow

Biyo bayan shawarar da Dr. Ahmad Gumi ya bayar, Gwamnatin tarayya tace ta fara magana da kasar Turkiyya dan su taimakawa Najeriya magance matsalar tsaro

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, sun tuntubi kasar Turkiyya dan ta taimakawa Najeriya wajan magance matsalar tsaro.

Ya bayyana hakane yayin ganawa da kungiyar Kiristoci ta CAN a ziyarar data kai masa a fadarsa dake Abuja.

Shugaban yace akwai bukatar Kiristoci su taya Najeriya da Addu’a dan kawo karshen matsalar.

Ya kuma kara da cewa, sun siyi Jiragen yaki 3 daga kasar Amurka amma ba zasu zo da wuri ba.

Hakan na zuwane bayan da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta yi watsi da kasar Amurka ta koma neman taimakon tsaro daga kasashen China, Pakistan da Turkiyya.

Karanta Wannan  Bincike: Karanta Jadawalin jihohin da aka fi samun matan aure na aikata Zìnà, 'yan mata ma na lalata, Rahoton yace babu irin wadannan matan ko daya a jihohin Jigawa, Katsina da Kebbi sannan Kuma jihar Taraba ce ta daya a Arewa wajan aikata wannan masha'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *