Friday, January 2
Shadow

Wata Sabuwa: An gano cewa Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga Bashin Manoma da CBN suka bayar Lokacin Buhari, da Kudaden Abacha da aka dawo dasu da kuma Paris Club

Rahotanni sun bayyana cewa, Naira Biliyan 200 da EFCC ke zargin Tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami da sacewa, ya samesu ne daga kudaden bashin da babban bankin Najeriya, CBN ya baiwa manoma bashi lokacin Buhari.

Da kuma kudin Abacaha da aka dawo dasu Najeriya da kuma kudin Paris Club watau bashin da Gwamnatin Tarayya da gwamnoni suka ciwo.

Kafar The Cable tace ta samu cewa Abubakar Malami ya sa matarsa me suna Hajiya Bashir Asabe ta ci bashin na manoma har Naira Biliyan 4 wanda kuma bata biya ba.

A yanzu dai EFCC sun sakata cikin wadanda za’a gurfanar dasu a gaban kotun tare, a baya dai Hutudole ya kawo muku cewa akwai dan Abubakar Malami da shima yanzu EFCC ke tuhuma.

Karanta Wannan  Hadisi ya tabbatar da cewa, Ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) akan masu aikata manyan zunubaine, shiyasa nace ina son in shiga Aljannah ba da ceton Annabi ba>>Dr. Hussain Kano

A bangaren Kudaden Abacha da aka karbo, lauyoyi turawa aka dauka suka yi aiki, amma rahotan yace Abubakar Malami shima ya dauki sabbin lauyoyi duk da cewa an kammala komai kudin kawai za’a bayar amma Malami yasa Lauyoyin suka yi aikin Boge aka biyasu dala Miliyan $16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *