
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sakawa kasafin kudin shekarar 2026 hannu a yau, Laraba.
Kasafin kudin na Naira Tiriliyan 1.4 ne wanda hakan ya samu halartar manyan jami’an Gwamnatin Kano.
Saidai rashin ganin mataimakin Gwamnan jihar a wajan ya jawo cece-kuce.
Dama dai wata majiya tace Gwamna Abba shi kadai zai koma APC ba tare da mataimakin gwamnan ba.
Hakanan a dazu ne muka ga Abba ya gana da shuwagabannin jam’iyyar APC na jihar Kano.