Saturday, October 17
Shadow

Da Sunana Samuel, Amma Na musulunta na koma Mohammed>>Inji Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume daga jihar Borno yace shi da iyayensa duk musulunta suka yi.

Yace ya taso a matsayin Kirista kuma ya je makarantar Kiristoci.

Sannan yace a da sunansa Samuel amma aka ce ya je ya shiga Musulunci ya koma Mohammed, sannan yace mahaifiyarsa ma tana cikin matan zumunta amma daga baya duk sun musulunta.

Saidai yace a gidansu raba kafa aka yi, wasu suka zama musulmai, was suka zama Kirista ta yanda duk inda ta fadi sha.

Karanta Wannan  Hukumar 'yansandan Najeriya ta saka tarar Naira Dubu Hamsin ga matasa masu shigar banza

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *