Monday, December 16
Shadow

Sakon rashin lafiya ga masoya

Allah ya baki lafiya masoyiyata.

Ina fatan wannan rashin lafiya ta zama kaffara ga zunubanki.

Rashin lafiya ka iya zama Alheri ta hanyar kankare zunubai idan mutum ya dauka cewa kaddara ce daga mahalicci ba wanine ko rashin wayonsa ne ya dora masa ba, ina fatan kina da wannan yakini dan samun amfanin wannan dama.

Cuta ba mutuwa bace masoyiyata ki koma ga Allah da neman gafarar zunubai.

Kullun ina sakaki a addu’a Allah ya baki lafiya masoyiyata.

Masoyiyata ki daure ki tashi, Dan amfanin kanki da sauran na kusa dake.

Masoyiyata insha Allahu zaki warke, ki yi imani da Allah da kuma fatan cewa zai baki Lafiya.

Karanta Wannan  Hirar soyayya

Masoyiyata ba zan iya jure rashinki ba, Insha Allahu kina daf da samun lafiya.

Duk runtsi duk wuya ina tare dake, wannan rashin lafiya jarabawace wadda kuma zata wuce ki warke insha Allahu.

Ki daina tunanin mutuwa, shi zafin ciwo yakan zo kuma ya wuce insha Allahu zaki warke.

Ni na dauki rashin lafiya a matsayin wata jarabawa da kuma tuni cewa mutum ya koma ga Allah dan neman yafiyar zunubai, masoyiyata ki koma ga Allah ta hanyar istigifari da neman lafiya insha Allah zaki warke.

Naga jikinki da alamar sauki, insha Allahu kwanannan zaki warke.

Masoyiyata akwai wani abu dana tanadar miki amma sai kin warke zan bayyana miki shi, Insha Allahu waraka na nan tafe.

Karanta Wannan  Sunayen soyayya na mata

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *