
Rashin Tabbas bayan kammala karatu da tsadar Rayuwa tasa yanzu iyaye sun fara tura ‘ya’yansu koyan aikin hannu
Rahotanni sun ce iyaye a yanzu sun fara hakura da maganar sai 'ya'yansu sun samu aikin Gwamnati da daukar albashi me tsoka.
Inda aka fara tura yara koyon sana'a yayin da suke zuwa makaranta a lokaci guda.
Rahoton wanda jaridar Vanguard ta hada, yace yanzu yara tun daga shekara 10 ana fara turasu zuwa koyon aiki dan su dogara da kansu da kaucewa matsalar su kammala karatu ya zamana sun zauna babu aikin yi.
Wasu kuma na tafiya da 'ya'yan nasu ne wajan aikin da suke dan su rika koya musu da wuri.
Lamarin matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ya zama ruwan dare inda dubbai sun kammala karatu amma basu samu aikin zama a ofis ba.