Friday, January 9
Shadow

Kotu ta bayar da Umarnin EFCC ta rike kadarorin Abubakar Malami 57

Kotun tarayya dake da zama a Abuja ta amincewa hukumar EFCC ta ci gaba da rike kadarorin tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami.

Kotun tace EFCC ta rike kadarorin guda 57 na wucin gadi kamin a amince a kwacesu na dindindin.

Hakanan Kotun ta bayar da belin Malami da dansa da matarsa.

Hakanan a zaman kotun, Mai Shari’a, Justice Emeka Nwite ya Gargadi Lauyan Abubakar Malami cewa kada ya sake yace zai nemi wata Alfarma a wajansa.

Yace ba zai lamunce a bata masa suna ba kuma duk sanayyarsa da mutum idan aka zo wajan aiki zai nuna ba sani ba sabo.

Karanta Wannan  Sharudan Komawar Kwankwaso shine, za'a bashi mataimakin shugaban kasa, Amma Kuma Gandujene zai kawo wanda za'a baiwa Gwamnan Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *