
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nemi wadanda zai baiwa mukaman Siyasa masu gaskiya da kishin Najeriya irinsa amma ya kasa samu.
Hadiminsa, Malam Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a wata hira da Ali Jita yayi dashi.
Yace Buhari ya gaya musu cewa a tsawon lokacin da ya dauka yana kokarin neman Mulki, ya manta bai nemi mutane nagartattu ba da zai yi aiki dasu.
Yace sai bayan da ya ci zabe, ya je gida ya kwanta amma Bacci ya ki zuwa, yace sai ya tuna wata ma’aikata da ke da matsala, sai yayi tunanin wanene zai dakko me irin ra’ayinsa ya baiwa wannan ma’aikata amma sai ya kasa samun ko da mutum daya.
Yace a wannan lokacinne yasan cewa bai samarwa kansa abokan aiki ba.