Monday, January 12
Shadow

A yau ne Gwamna Abba zai koma APC a hukumance

Rahotanni sun bayyana cewa, a yau ne, 12 ga watan Janairu, Gwamman Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC a hukumance.

A baya dai an saka ranar 5 ga watan Janairu cewa ranar me Abba zai koma APC amma hakan bata samu ba.

Saidai daga baya an bayyana 12 ga wata, watau yau, kenan inda aka ce Abban zai koma APC.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon shugaban jam’iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta dawo Najeriya daga Dubai dan halartar wannan bikin na komawar Abba APC.

Karanta Wannan  Atiku Abubakar yayi magana kan rade-radin da ake cewa, ya baiwa Soja, AM. Yerima dankareriyar motar Alfarma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *