
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa, zaben da ‘yan Najeriya ke yi bashi ke sa mutum ya ci zabe ba.
Ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV.
Ya bayyana cewa, ‘Yan siyasa na yin dukkan abinda suke tunani da zai basu nasara.
Hakanan suma jami’an zabe wajan tattarawa da aika sakamakon zaben akan samu wasu suna yin magudi.
Tambuwal yace yana goyon bayan duk wani canji da za’a kawo a harkar zabe wanda zai inganta harkar.