
Matar tsohon gwamnan Kaduna, Hajiya Hadiza Ismail El-Rufai ta bayyana amincewa da kalaman gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda.
Dikko ya bayyana cewa babu wani jin dadi a zama gwamna, mutane na ganin kamar jin dadi suke amma a zahiri wahala suke sha.
Ya kara da cewa ko da kasashen waje da suke zuwa, saidai ai ta taruka ba shakatawa suke zuwa yi ba.
Hajiya Hadiza da take martani akan kalaman na Gwamnan Katsina, ta bayyana cewa, shima mukamin matar Gwamna haka yake.