
Wasu ‘yan Najeriya da suka je kallon wasa a kasar Morocco sun yi rikici da hukumomin dake kula da filin wasan da aka buga jiya tsakanin Najeriya da Morocco.
Sun shiga filin da wuri inda suka samu wuri suka zauna amma sai masu kula da filin wasan suka ce su tashi daga wajan su canja wajan zama.
Saidai sun ce ba zasu tashi ba inda suka dauki abin suka watsa a Duniya.
Sun yi zargin ana son a nuna musu banbanci ne da kaisu inda ba zasu iya baiwa Najeriya goyon bayan da ya kamata ba.
A karshe dai masu kula da Stadium din sun kyalesu.