Masana masu sharhi akan al’amuran yau da kullun sun bayyana cewa, ko da matatar man Dangote ta fara aiki ba lallai tasa farashin man fetur ya sauka ba.
Masanan aun bayyana dalilan cewa,har yanzu matatar ta Dangote daga kasashen waje take samo danyen man da tame tacewa.
Sannan farashin dala dake ta kara hauhawa shima ba lallai ya bayar da damar samun saukin man fetur din ba ko da mamatar ta Dangote ta fara aiki ba.
A kwanannan dai Dangote ya bayyana cewa zai ci gaba da shigo da danyen man fetur daga kasar Amurka saboda rashin isashshen danyen man fetur din a Najeriya.