Monday, January 19
Shadow

Ji dalilin da ya hana Abba Kabir Yusuf komawa jam’iyyar APC

A yayin sa labarai suka bayyana cewa, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai koma jam’iyyar APC daga NNPP, har yanzu komawar tasa bata tabbata ba.

Sau biyu kenan ana daga shirin komawar Abba APC saboda wata matsala.

Rahoton yace, Dalilin da ya hana abba komawa jam’iyyar APC shine bukatun da ya gabatarwa da jam’iyyar ta APC wanda ita uma har yanzu bata amince dasu ba.

Jaridar Thisday tace Gwamna Abba ya bukaci APC ta bashi tabbacin samun tikitin takara a 2027 ba tare da hamayya ba, hakanan ya bukaci a bashi damar aika sunayen wadanda za’a baiwa Ministoci zuwa Gwamnatin tarayya.

Saidai wani dake kusa da Tsohon gwamnan jihar kuma tsohon shugaban jam’iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa akwai gwamnoni da yawa da suka koma APC wadanda basu nemi wadannan bukatu ba.

Karanta Wannan  Babu wani Butulci dan Abba ya koma jam'iyyar APC >>Inji Malam Ibrahim Shekarau

Saidai yace har yanzu ana ci gaba da tattaunawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *