
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya jewa Malam Haruna na Chiranchi Dirayi da akawa iyalansa aika-aika gaisuwa.
A yayin ziyarar gwamnan ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ta dauki nauyin rayuwar Malam Haruna Chiranci Dorayi gaba daya.
Sannan an biya masa hajji da Umara, sannan za’a dauki nauyin yi masa aure idan ya samu wadda yake so.
Sannan an bashi kyautar gida.
Sanna Gwamnan ya sha Alwashin zartas da hukuncin da kotu ta yankewa wanda ake zargi a lamarin.
Hakanan yace duk ma wasu da aka samu da hannu a irin wannan abu zai saka hannu a zartas musu da hukunci.