
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya koka da cewa, an fara magudin zaben shekarar 2027.
Ya bayyana hakan a shafinsa na sada zumunta inda yace an fara hakannne ta hanyar kaucewa gyaran dokar zabe.
Ya zargi majalisar tarayya da kaucewa gyara dokar zabe wadda zata sa kada a maimaita kuskuren da aka tafka a zaben shekarar 2023.
Atiku yace idan ba’a gyara dokar zaben ba ba lallai a samu sakamakon zabe sahihi a zaben shekarar 2027 ba.