
Tauraruwar fina-finan Hausa, Rashida Mai Sa’a Ta dauki hankula sosai bayan da ta bayyana cewa masu sukar dan makullin da take sayarwa matan aure dake hana mazansu neman mata a waje mazinata ne.
Rashida ta samu Raddi daga masu fadakarwa a kafafen sada zumunta irin su Baffa Hotoro da Dr. Hussain Kano inda suka bayyana abinda take yi da cewa shirkane.