Tuesday, February 3
Shadow

Da Duminsa: A yayin da ake rade-radin cewa, Gwamnatin Kano zata sauke Sarki Muhammad Sanusi II daga Sarauta, Gwamna Abba ya bayyana matsayarsa kan lamarin

A ‘yan kwanakin nan, Rade-radi, musamman a kafafen sada zumunta sun yadu cewa, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf zai sauke Sarki Muhammad Sanusi II daga sarautar Kano.

Hakan na zuwane bayan da Abban ya koma jam’iyyar APC.

Hakanan Kwamishinan yada labarai na Kano, Ibrahim Waiya ya bayyana cewa, za’a kawo karshen rikicin Masarautar ta Kano ta hanyar lalama da ganawa da masu ruwa da tsaki.

Wannan yasa wasu suka rika hasashen cewa, wai za’a sauke me martaba, sarkin Kano, Muhammad Sanusi II daga Sarautar Kanon.

Saidai a wani Sabon Rahoton da Daily Trust ta ruwaito, tace, Abba yace Sarki Muhammad Sanusi II ne zai ci gaba da zama sarkin Kano, ba za’a tsigeshi ba.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa Kalli Bidiyo: Inda wasu ke ikirarin diyar Annabi(Sallallahu Alaihi Wa Sallam) Nana Fadima(AS) ta bayyana a bangon dakin wata mata a garin Zauro na jihar Kebbi

Hakan ya fito ne daga bakin me magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature, a wata hira da yayi da Daily Trust.

Yace canja jam’iyya da Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi, ba zata taba Masarautar Kano ba.

Yace sarautar Kano ba harka ce ta siyasa ba, bangare ne na Al’ada wanda babu ruwansa da harkar siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *