Friday, January 23
Shadow

Kalli Abincin da ake baiwa Mahajjata a kasar Saudiyya: Mahajjatan sun koka inda suka ce duk da biyan Naira miliyan 8 a matsayi kudin aikin hajjin bana abincin da ake basu kenan

Mahajjatan Najeriya a kasar Saudiyya sun koka da kalar abincin da ake basu duk da biyan Naira Miliyan 8 a matsayin kudin aikin hajjin bana.

Daya daga cikin mahajjatan me suna Babagana Digima ne ya wallafa hoton kalar abincin da ake basu a shafinsa na facebook.

Abincin dai koko ne da kosai guda 3.

Babagana Digima ya kara da cewa, mahajjata yanzu sun koma bara dan neman abinda zasu ci saboda kudinsu dala $300 daya rage daga cikin dala $500 da suke da ita har yanzu ba’a basu ba.

Hukumar Alhazai ta kasa, National Hajj Commission of Nigeria (Nahcon) da take martani akan lamarin, tace ta sa a yi bincike kan lamarin.

Karanta Wannan  Hukumar kula da birnin tarayya Abuja zata sake gina sabuwar Hukumar zabe me zaman kanta INEC, 'yan Najeriya da yawa sun ce wata hanyar bata kudi ce

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *