Babbar hanyar da mace take gane tana da ciki shine ta hanyar gwaji.
Akwai hanyoyin gwaji da yawa amma mafi inganci itace zuwa Asibiti ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake kira da pt strip test a gida.
Ana iya samun tsinken gwaji a kemis da yawa kuma bashi da tsada, saidai dan samun sakamako mafi kyawu a bari sai bayan kwanaki 10 ko 14 a kamin ayi gwajin cikin bayan yin jima’i, wasu masana ma na cewa a bari sai bayan kwanaki 21 kamin a yi gwajin cikin.
Inda wasu kuma ke cewa a bari sai bayan an yi batan wata, watau idan lokacin zuwan jinin al’ada yayi amma ba’a ganshi ba.
Ana kuma amfani da hanyoyin gargajiya da yawa wajan gwajin ciki kamar amfani da gishiri, suga, da sauransu amma dai yin amfani da tsinken gwaji yafi tabbas ko kuma aje asibiti.
Akwai alamun shigar ciki da mace zata iya gani irinsu:
Jiri
Amai
Yawan fitsari.
Zazzabin safe.
Kasa cin abinci yanda aka saba da sauransu.
Saidai duka wadannan alamu basu bayar da tabbacin ciki sai an yi gwaji.