
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Alkali Zaria ya fitar da sanarwa kan dakatarwar da kungiyar Izala ta masa.
Ya fitar da sanarwar ne a shafinsa na Facebook.
Ga abinda yace kamar haka:
“Aslm Alkm wrhmtlh wbrkth magana Ta gaskiya shine fadin Allah s w t da sannu zakuyi ta son Abu ba Alkhairi bane Agareku saannan da sannu zakuyi ta kin Abu kuma shine Alkhairi gareku Allah shine mafi sani Alhali mu bamu sani ba inaso kowa ya sani Ni Dan kungiyar jamaatu izalatil bid.ah wa ikamatis Sunnah ne NHQ jos Karkashin Jagoranchin Fhadilatush sheikh Muhammad sani Alhaji Yahaya Jengre Sannan kuma ba Nine Na kai kaina Damaturu ba kungiya ce ta Turani Amatsayin me Tafseer Na wannan Shekarar 1447 /2026 Duk Dan wannan kungiya Ta Jamaatu izatil Bid.ah Waikamatis Sunna ya sanmu da Daa da biyayya bisa ga dukkan umurni da Aka bamu matukar bai saba ma shariar Allah da manzansa s a w ba kuma Na karbi wannan umurni Na shugabanmu Babanmu Malaminmu fadilatush sheikh Muhammad sani Yahaya Jingre da sunan Allah . Allah ka bamu ikon yin biyayya akan kitabu was.sunnah tsakaninmu da Allah s w t yan uwana da Abokaina masoya da kowa da kowa ina me baiwa kowa hakuri Akan wannan Al Amari waadin da Allah ya Rubutomin dazanyi A Damaturu iya lokachin da Allah ya kaddara min kenan Agarin Damaturu Daga karshe inaso mu zamo masu daa da biyayya domin duk wata nasara tana tareda da daar da biyayya Allah yasa haka shine mafi Alkhairi Agaremu Duniya da Lahira Nagode sosai Allah ya hadamu A Aljanna”