
A yaune dai ICPC ta mayar da Malam Nasiru Ahmad El-Rufai babbar kotun jihar inda ake masa shari’a game da zargin Almundahanar kudade.
Saidai kotun tace zaman kotun ba zai yiyu ba saboda dayan wanda ake musu shari’ar tare da malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai zo ba saboda bai da lafiya kuma shari’ar ta mutum biyu ce dan haka ba zai yiyu a ci gaba da ita ba sai yana nan.
A yanzu za’a tafi da malam Nasiru Ahmad El-Rufai zuwa babbar kotun tarayya inda za’a saurari neman belin da yayi.
KARIN BAYANI:
An kuma je babbar kotun tarayya inda El-Rufai ya shigar da korafin neman beli, saidai an daga ci gaba da sauraren karar har sai nan da 1 ga watan Afrilu