Wednesday, April 1
Shadow

Jam’iyyar ADC ka iya samun Tangarda: Hukumar zabe me zaman kanta INEC ta cire Shugaban ADC na rikon kwarya da sakataren jam’iyyar na Rikon Kwarya daga shafinta

Hukumar zabe me zaman kanta, INEC ta sanar da cire shugaban jam’iyyar ADC na rikon kwarya, David Umahi da sakataren jam’iyyar na rikon kwarya, Rauf Aregbesola daga shafinta na tattara bayanan shuwagabannin jam’iyyun Najeriya.

INEC tace ta yi hakanne saboda karar da aka shigar a kotun daukaka kara daga wani bangare na jam’iyyar da basu yadda da shugabancin su David Mark ba.

Kwamishinan yada labarai na INEC, Mohammed Kudu Haruna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, yace zasu dakata har sai sun ji hukuncin da kotun daukaka karar zata yanke.

Wanda ya shigar da karar shine Nafiu Bala Gombe wanda ke ikirarin cewa shine shugaban jam’iyyar ta ADC.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Shugaban NNPLC ya koma bakin aiki yayin da ake rade-radin an koreshi saboda zargin yana munafurtar shugaban kasa yana taimakawa 'yan Adawa watau su Atiku Abubakar, saidai wata majiya tace Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ce ta hana a koreshi daga aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *