
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya sanar da bayar da tallafin Naira Biliyan 20 a cikin gidauniyar da matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kaddamar
Dangote yace zai bayar da kudadenne a cikin shekaru 5 masu zuwa.
Ya bayyana hakane a wajan kaddamar da wannan gidauniya.
Gidauniyar an kafatane dan samar da abinci ga marasa karfi.
Hakanan kamfanin NNPCL ya bayyana cewa, shima zai bayar da tallafin Naira Biliyan 10 cikin shekaru 5 masu zuwa.