
A ziyarar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya kai jihar Filato an jiyoshi yana cewa babu lokaci, idan ya ci gaba da magana, ba lallai su iya komawa Abuja ba.
Ya kara da cewa kuma a Jos babu inda zasu iya kwana, inda ya karkar maganarsa da wannan kalamai ya zauna.
Wannan kalamai nasa dai sun jawo cece-kuce inda ake ganin basu dace ba.
A baya dai shugaban yace garin Jos ba wutar lantarki inda yace kuma mintuna goma zasu yi su koma.
Shugaban yaki shiga cikin garin Jos inda a filin jirgi ya tsaya saidai aka kai masa iyalan wadanda suka jikkata ya gana dasu a filin Jirgin.
Hakan ya jawo masa suka sosai cikin wadanda suka sokeshi hadda tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Saidai fadar shugaban kasa tace, shugaba Tinubu bai shiga cikin garin Jos bane saboda babu wuta a filin jirgin Jos din kuma idan suka kai dare, jirginsa ba zai iya tshi ba.