Friday, December 5
Shadow

An ji harbin bindiga a kusa da fadar sarkin Kano

Rahotanni sun bayyana cewa, ranar Litinin an ji karar harbin bindiga a kusa da karamar fadar sarkin Kano dake Nasarawa.

A nan ne dai Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune inda ya kafa fadarsa bayan da aka saukeshi daga sarautar Kano.

Rahoton Premium Times yace an yi harbinne dan hana kama Aminu Ado Bayero wanda kotu ta bayar da umarnin fitar dashi daga fadar ranar Litinin.

Wannan harbi da aka yi yasa mutane suka rika canja hanya suna komawa da baya.

Rahoton yace ba’a tabbatar da ko jami’an tsaro ne ko masu tsaron fadar bane suka yi harbinba.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Ana zargin kwaikwayar sa hannun Babban alkalin kotun Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya wanda yace a sauke Sarki Sanusi II daga kujerar sarautar Kano, Kalli Hotunan dake tabbatar da hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *