Wata babbar kotu a Kano ƙarkashin jagorancin mai shari’a Amina Aliyu ta hana ‘yan sanda, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS da sojojin Najeriya daga korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ko fitar dashi daga fadar Sarki.
Majiyar mu ta a yau ta ruwaito Sarkin ne ya shigar da ƙara tare da majalisar masu naɗin sarakunan Kano su hudu: Madakin Kano Yusuf Nabahani; Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi; Sarkin Bai Mansur Adnan da; Sarkin Dawaki Maituta Bello Tuta.
Menene ra’ayinku kan wannan turka-turka na sarautar Kano?