
Malamin addinin Islama, Farfesa, Mansir Isa Yelwa ya bayyana cewa, a yanzu ya janye kalamansa na cewa zai daina jan limanci a masallacin ATBU.
Yace ya dauki wannan mataki ne bayan da iyaye, da malamai da abokan afziki suka saka baki a lamarin.
Malam a baya yace ya bar limanci a masallacin ATBU ne saboda an ce za’a warewa ‘yan darika masallacin su a makarantar.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce da zazzafar Muhawara.