Wani mutum a kasar Afrika ta kudu ya mutu a dakin Otal bayan yin fasadi da karuwa.
Matan dake gidan karuwan sun dakata da aiki bayan faruwar lamarin da ya girgizasu.
Rahoton yace bayan da suka gama abinda zasu yi, karuwar ta taba mutumin inda ta ga ya mutu baya motsi.
Anan ne aka kira jami’an tsaro dana lafiya inda suka tabbatar da cewa ya mutu.
Ana bincike dan gano abinda yayi sanadiyyar mutuwarsa.