Thursday, August 27
Shadow

Kalli Bidiyon: Ganin Habiba Dorayi a ofishin Gwamnan Kano ya jawo cece-kuce

Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta dauki hankula bayan da aka ganta a ofishin Gwamnan jihar Kano.

Habiba wadda ta shahara wajan yin kalaman batsa a kwanannan an ganta tana tallata gwamnatin Abba Kabir Yusuf inda ta hada wata kungiyar mata ‘yan Tiktok me suna Kano First Tiktokers wanda suke tallata Gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

‘Yan Fafutuka na Kafafen sada zumunta sun nuna fushinsu inda suka ce su da suka dade suna tallata Gwamnatin Kanon basu taba zuwa ofishin Gwamna ba amma ita gashi daga baya tazo ta shiga gabansu.

Karanta Wannan  Da Duminsa: Na fasa ziyarar da na yi niyyar kaiwa jihar Ogun, saboda abinda ya faru a jihar Filato>>Inji Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *