
Tauraruwar Tiktok Habiba Dorayi ta dauki hankula bayan da aka ganta a ofishin Gwamnan jihar Kano.
Habiba wadda ta shahara wajan yin kalaman batsa a kwanannan an ganta tana tallata gwamnatin Abba Kabir Yusuf inda ta hada wata kungiyar mata ‘yan Tiktok me suna Kano First Tiktokers wanda suke tallata Gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
‘Yan Fafutuka na Kafafen sada zumunta sun nuna fushinsu inda suka ce su da suka dade suna tallata Gwamnatin Kanon basu taba zuwa ofishin Gwamna ba amma ita gashi daga baya tazo ta shiga gabansu.