
Tsohon dan majalisaf wakilai, Hon. Ehiozuwa J. Agbonayinma ya nemi EFCC ta dawo da binciken cin hanci da rashawa na shekarar 2006 da tawa Atiku Abubakar.
Ya nemi cewa ya kamata a dawo da binciken kuma a hukunta Atiku Abubakar idan an sameshi da laifi.
Saidai Jaridar Leadership ta nemi jin ta bakin hukumar EFCC amma wasu ma’aikatan hukumar da sukace suna son a sakaya sunayensu, sun ce hukumar ba zata binciki Atiku Abubakar ba musamman ganin yanda lamarin yayi kusa da zaben 2027.
Atiku Abubakar yace wannan maganar banzace kamata yayi Gwamnati ta mayar da hankali wajan magance matsalolin ‘yan Najeriya ba yi masa bita da kulli ba.