
Hajiya Khadija dake aiki a kasashen Larabawa ta bayyana yanda suke fama da Larabawan wanda labarin nata ya dauki hankula
Tace akwai gidan aikin da za’a kaika kwata-kwata basa sallah.
Tace idan suka ganka kana Sallah, sai su rika maka kallon wani waliyyi, su rika cewa ka musu addu’a.
Sannan tace akwai kuma inda suke Sallar su kuma Dan kana sallah zasu iya wucewa ta gabanka, ko kuma kana tsaka da sallah su rika maka magana kuma suna jira ka basu amsa