Hukumar ‘yansandan Najeriya ta bayyana cewa, duk wani dansanda dake hutu ya koma bakin aiki.
Wannan mataki na zuwane yayin da ake kusa da fara Zàngà-zàngàr kukan tsadar rayuwa a Najeriya.
Hakanan sanarwar ta bayyana cewa, kada a sake a samu wani dansanda da shan giya dan kada yayi tambele a wajan zanga-zangar.
Hakanan an bukaci duka ‘yansanda dasu saka kayan aiki cikakku a goben kuma an dakatar da kowane irin hutu.