Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ne ya ayyana dokar a taron manema labarai da ke gudana a gidan gwamnati a halin yanzu.
Ya ce an saka dokar ne domin a dakile sace-sace da fashe-fashen kayan gwamnati da na al’umma da wasu ɓatagari ke yi a ƙarƙashin zanga-zanga.
Ya ce wasu ƴan siyasa ne da ba sa don ci gaban Kano ke daukar nauyin yan daba wadanda su ka dake da zanga-zanga su ka fara kai hare-hare.
Ya kuma umarci jami’an tsaro da su gaggauta fara aiwatar da dokar nan take.