Monday, December 16
Shadow

Amfanin tumfafiya

KADAN DAGA CIKIN AMFANIN BISHIYAR TUMFAFIYA

Sharadin Shine Ayi Sharing Domin Yan uwa su Amfana

Daga Dr. Nura Salihu Adam _Salihannur”

+2347048008080
+2348023110225

SAIWAR TIMFAFIYA?

  1. Tana cutarwa kamar (poison) ce dan haka kada a kuskura a sha,yanda ake sarrafata dan magani da ita baya da alaqa da maganin da za a jiqa a sha a ruwa ko ga wani abin sha. Ana amfani da ita ga wanda maciji ya ciza

ANA AMFANI DA??

  1. Bawon tumfafiya ko itatuwan waton stems a turance kenan dan maganin cutar kuturta (leprosy).za’a dake itatuwan a nemi man kade a kwa6a sai a shafa a inda cutarta ta bayyana.

ANACIN KWALLON DAKE CIKIN??

  1. Furen tumfafiya.Idan aka bude fulawar za’a ga wannan dan kwallon a cikin furen tumfafiya to shi za’a ci ba dukkanin flower ba. yana maganin kamin mugu waton mayu kenan.Wallahi basa qaunar ruhi da jinin mai cin furen tumfafiya.Idan zaku lura zaku ga akwai wata fara da ake samu ga tumfafiya kadai mai launin kore,ita wannan farar bata da abincin da ya wuce wannan flower dake a tumfafiya.Ita ma magani ce sosai na karya sihirin maye da maitarsa.
Karanta Wannan  Alamomin ciwon ulcer

ANA GAURAYA??

  1. Bawon bishiyar tumfafiya da garin habbat sai a turare ko wane lungu ko daki,ko gida ko duk wani waje da ake bukata.Wannan na korar baqaqen iskoki da miyagun qwari kamar macizzai da makamantansu.

ANA GAURAYA??

  1. Garin ganyen tumfafiya dana lalle a kwa6a a shafa a inda ciwo yake.Yana maganin cutukan cin ruwa,tsagewar yatsa,ciwon yatsa na dan kakkarai.

ANA DIGA??

  1. Madarar tumfafiya wacce idan aka 6allo ganyenta za a ga madarar tana zubowa.Za’a karkare makero da dutse sai ya karkaru sai a diga a saman makeron,a fake yin haka a duk kwana biyu.

MACE WADDA TAKE??

  1. Mafarkin iska yana zomata yana saduwa da ita ta nemi saiwar tumfafiya da kunnen gamji da garin habba ta tirare gabanta dasu.Amma kuma da sharadi idan akwai ciwon mara ko yankewar jini,ko shigar ciki,ko macen da ta haihu ko take cikin jinin al’ada sai ta nemi karin bayani.
Karanta Wannan  Yadda ake gwajin ciki da gishiri

AITARIN FUKA??

  1. Na asthma, ya nemi 6awon tumfafiya ya shanya su bushe ya cinna masu wuta yayi tirare.

TSUTSAR CIKI

  1. Tsutsar ciki – A nemi furen ayi

Daga Dr. Nura Salihu Adam _Salihannur”

AMFANIN FUREN TUMFAFIYAH

1–Farin Jinin Samari Ko Farin Jin Yammata,
Asha Garin Furen Tumfafiya da Nono Ranar Lahadi Bayan idarda Sallar Asuba,

2–Kwarjini da Haiba
Ka Sa Furen Tumfafiya Cikin Aljihun ka Ka Shiga Cikin Jamaa Ka Gani

3–Jefa Soyayyah Cikin Zuciyar Saurayi Ko Budurwa
Aci Furen Tumfafiya Wanda Bai Buda ba adadin Haruffan Sunan Saurayin da ake so a Jefa Soyayyar Zuciyar Shi Ko Budurwar,
Misallin idan Sunan Shi Nuhu ne Kaga Haruffan asunan Shi 3 Kenan, Aishatu 4,

Karanta Wannan  Maganin matsi ciki da waje

4–Ana daka Garin Furen Tumfafiya a Shi Ckin Hoda idan, Macce ta Shafa Zata dau Hankali Sosai, Amma Macce Ta Kiyaye

5–Cin Furen Tumfafiya Yana Qara Qarfin Namiji Sosai

6–Ana Daka Danyen Furen Tumfafiya Ayi Wanka da Shi Maganin Farin Jini

7–Wadda ta Dade Tana Neman Miji Abu ya Gagara
Ta Rubuta Alamnasharaha Qafa 3 Tasa Garin Furen Tumfafiya ciki Tasha Allah Zai Kawo Mata Nata

8–Matar da Ta Rasa Zaman Lafiya da Mijinta Kullun Cikin Rashin Zaman Lafiya, Idan dai Ba Halin ta bane ko na Mijin,
Tayi Hayaqi da Furen Tumfafiya, daga Ranar Ba Mai Qara Jin Tsakanin Su

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *