Ana dan diga Lemun tsami a cikin kwai dan a gyara dandanon kwan, musamman idan za’a soyashine.
Hakanan wannan hadi yana taimakawa kwan ya soyu da kyau ta yanda duka sinadaran da ake bukata zasu fito ba tare da wata illa ba.
Saidai ba’a son ruwan lemun tsamin ya zamana yana da yawa wanda za’a zuba.
Masana sun bayar da shawarar a zuba rabin karamin cokali na ruwan lemun tsami idan za’a soya kwan, ko kuma ana ina matsa lemun idan ya diga sau 3 ya isa.
Hakan bashi da illa, kamar yanda masana kiwon lafiya suka sanar.