Thursday, October 3
Shadow

Amfanin habbatussauda

AMFANIN HABBATUSSAUDA WANDA YA KAMATA KU SANI.

Idan kun karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.

Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye da yawa, misali ana kiranta da “Habbatul Baraka” da larabci, wato kwaya mai albarka. Da turanci kuma ana kiran ta da ‘the blessed seed’, Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu.

Binciken ya dangata habbatus-sauda da matukar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka.

Ana samun Habbatus-sauda daga ‘ya’yan tsiron “Nigella sativa”. Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar al’ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma magance wasu cututtuka dake addabar jikin dan-adam.

Karanta Wannan  Amfanin goruba

Ba tare da bata lokaci ba, ga jerin magunguna 31 da ake samu daga wannnan tsiro mai albarka, da fatan a sha karatu lafiya, sannan da fatan za’a jarraba domin gane wa ido amfaninta.

  1. Matsalar Tsakuwar Koda/Mafitsara; Ana amfani da Habbatus Sauda domin fitar da tsakuwar koda ko ta mafitsara. Yadda za a hada wannan maganin shine, a samu habbadus sauda mai kyau, da kuma zuma marar hadi, sai a cakuda su sannan a zuba ruwan zafi a rinka sha. Da yardar Allah za a samu waraka. Hakanan za a iya amfani da wannan hadin don kawar da matsalar fitsari musamman ga maza tsofaffi dake fama da wannan matsala.
  2. Maganin Ciwon Kai; An tabbatar da cewa, ta na magance ciwon kai. Domin samun wannan fa’ida sai a hada garin habbatus-sauda da ruwan Kal, ake sha sannan kuma a dinga digawa a hanci don samun afuwa daga matsanancin ciwon kai.
  3. Samar Da Isasshen Ruwan Nono Ga Mace Mai Shayarewa; Wani lokacin akan samu mace ta haihu amma kuma ta rasa isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta, idan har haka ta kasance, sai a samu garin habbatus-sauda a hada ta da madara, mace mai shayarwar ta rinka sha, idan Alllah Ya yarda za ta samu isasshen ruwan nonon da za ta shayar da jaririnta.
Karanta Wannan  Amfanin shan ruwan kwai

Da sauransu Dayawa….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *