Ranar litinin, ‘yan Najeriya sun fara zanga-zangar nuna rashin jin dadi kan karancin man fetur a Abuja.
Kungiyar Coalition of Concerned Civil Society Organizations of Nigeria ce ta shirya zanga-zangar dan jawo hankalin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu kan ya magance matsalar karancin man fetur data kunno kai.
Shugaban kungiyar, Comrade Aminu Abbas y dora alhakin karancin man fetur din akan shugaban kamfanin man fetur na kasa, NNPCL, Mele Kolo Kyari.