Saturday, December 21
Shadow

Ji yanda wani me Adaidaita Sahu ya kashe mahaifiyarsa ya kuma yanke wasu sassan jikin dansa dan yin tsafi

Wani me adaidaita Sahi/Keke Napep ya kashe mahaifiyarsa sannan kuma ya yanke wasu sassan jikin dansa dan yin tsafi.

Mahaifiyar tasa ta ga ya yanki wasu sassan jikin dansa dan yin tsafi inda ta kaiwa dan nasa dauki anan ne a kokarin hanashi aikata wannan laifi ya kashe mahaifiyar tasa.

Ya tsere amma alhaki sai ya fada cikin wari rami yayin da yake gudu.

Sunan mutumin Amadi Alozie kuma lamarin ya farune a jihar Obingwa, karamar Obingwa a wani yanki da ake kira da Umudosi,kamar yanda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Tuni dai aka garzaya da dan nasa zuwa asibiti.

Karanta Wannan  Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II Ya Kai Ziyarar Ta'aziyyar Rasuwar Hajiya Dada 'Yar'Adua

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *