Kakakin Shugaban kasa,Ajuri Ngelale ya bayyana ajiye mukakinsa na magana da yawun shugaban kasa da kuma zama jakadan shugaban kasar a bangaren dumamar yanayi.
A sanarwar da fadar shugaban kasan ta fitar tace Ajuri ya mikawa shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa,Femi Gbajabiamila takardar ajiye aiki.
Yace dalilinsa shine yana son mayar da hankali wajan kula da lafiyar daya daga cikin iyalansa.
Ya bayyana cewa, hutune zai tafi amma wanda babu ranar dawowa sannan kuma wannan mataki ba dan yana so ya daukeshi ba.
Yace sai da ya shafe kwanaki kana shawara da danginsa akan lamarin.