Ana yin gwajin ciki da gishiri a gida dan gane ko mace na da ciki ko bata dashi.
Yanda ake yinshi shine:
Ana samun kofi ko mazubi a yi fitsari a ciki sai a zuba gishiri a ciki kamar chokali 2 zuwa 3.
Sai a barshi zuwa minti 1 ko 5.
Idan yayi ruwan madara ko yayi gudaji, to alamar mace na da ciki kenan.
Idan kuma ya tsaya a yanda yake ba tare da ya canja ba to baki da ciki.
Saidai shi wannan gwaji na gishiri bashi da inganci a wajen masana kiwon lafiya kuma babu wata hujja ta ilimi data tabbatar da sahihancinsa.
Hanya mafi inganci da ake yin gwajin ciki itace ta hanyar zuwa Asibiti a gwada mace ko kuma amfani da tsinken gwaji wanda ake cewa pt strip test. Mun yi rubutu kan yanda ake yin wannan gwaji: Yadda ake amfani da tsinken gwajin ciki
Tnx