Gwamnan jihar Zamfara a arewacin Najeriya ya ba wa wasu zaƙaƙuran dalibai 30 tallafin karatu domin su yi karatu a sakandiren gwamnatin tarayya ta Federal Government Academy da ke Suleja ta jihar Neja.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da yake ganawa da ɗaliban da kuma jagorancin Cibiyar Muhammad Kabir Danbaba Centre for Women and Youth Development Center a fadar gwamnatin jihar da ke Gusau.
Mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce cibiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen nasarar da jihar ta Zamfara ke samu a ɓangaren ilimi. Sanarwar ta ƙara da cewa yawancin ɗaliban da suka fi samun nasara na makarantun gwamnati ne.
“Wannan nasarar da kuka samu ta nuna cewa gwamnatinmu na ƙoƙari wajen inganta ilimi,” a cewar Gwamna Dauda Lawal.