Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindiga, Kachalla Baleri.
Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan inda yace an kamashine a Rouga Kowa Gwani.
Baleri wanda dan Shinkafine ya addabi mutane a Zamfara, Sokoto da Maradi.
Ya jagorancin kisan mutane da yawa da kuma garkuwa da mutane da yawa.
Yana daya daga cikin na hannun damar Kachalla Bello Turji kuma shine mutum na 40 mafi hadari da sojojin Najeriya suke nema ruwa a jallo.