Ga mata masu fama da kaikan gaba, ga dama ta yanda za’a iya magance matsalar cikin sauki.
A gida zaki hada maganin da kanki ba tare da kin sayi maganin ba. Kusan kowa zata iya hada wannan magani wanda kuma da yardar Allah za’a samu biyan bukata.
Ga yanda za’a hada maganin kamar haka:
MAGANIN ‘KAI’KAYIN GABA NA MATA DA ‘KURAJE
uwar gida zaki sama ruwan zafi ki zuba gishiri kiringa kama ruwa dashi.sannan zaki sami bagaruwa zaki tafasa sannan kiringa kama ruwa da lta wato ruwan yazama akwai dumi alokacin da zakiyi.bayan wannan zaki samu saiwar(bini da zugu)sai kuma saiwar(marke) sai(jar kanwa)ki hada kitafasa ki dinga sha to ln sha allahu zaki samu saukin ciwan mara da kuma kaikayin gaba dama sauran cututtukan da suka damu mata inda ta bangaran nanne kamar yadda masana sukace dan haka yar uwa ldan kinada wannan matsalar sai kiyi kokari wajan ganin kin samu wadannan saiwoyin kin tafasa da jar kanwa kina sha
kuma ba daga kin sha sau dayaKi daina shaba. a’a aibalokaci daya zakiga saukiba cuta ce kawai take shiga lokaci daya sauki kuwa sai ahankali.dan haka sai ki dage ki kuma gwada dafatan(ALLAH)ya bamu dukkan saukin lamuranmu.AMEEN
Ga kuma wasu shawarwari ga maza da mata masu fama da kaikan gaba
Matsalar kaikayin MATSE- MATSI, abu ne wanda yake
damun mutane da yawa
Maza da mata. Insha Allah zamuyi
bayanin yadda matsalar
take, da kuma yadda za’a
magance ta. Matsalar kaikayin gaba da
kaikayin matse-matsi tana
faruwa bisa dalilai kamar
haka:
1. Akwai wasu irin
Kwayoyin halittu na
bacteria wadanda suke
rayuwa ajikin ‘Dan Adam.
wasu daga cikin jikinsa,
wasu kuma daga waje akan fatarsa. Mafiya yawa daga cikin
wadannan Kwayoyin
Bacteria din bassu
cutarwa. amma akwai ‘Yan
Qalilan masu cutarwa. To su dai bacteria sun fi
son zama ne awajen da
yaje da damshi-damshi.
Kamar cikin dubura, ko
al’aurar mace, ko kuma
acikin matse-matsi. Taruwarsu acikin matse-
matsin mutum shi ke kawo
masa kaikayi awajen.
kuma da zarar mutum ya
sosa, sai fatar wajen ta
Qara yin kauri. sai kuma kaikayin ya Qaru. Da haka da haka duk
lokacin da kayi susa sai
fatar wajen ya Qara kauri
da damshi-damshi. Sai su
kuma bacteria din su ci
gaba da haihuwa awajen.
2. KYASBI (ECZEMA) Shi ma
idan ya kama fatar MATSE-
MATSI akan samu wannan
kaikayin.
3. KAURIN JIKI: Wato Qiba.
idan mutum yana da Qiba,
to dole zai rika yawan yin
gumi (zufa) kuma matse
matsinsa zai rika tara
damshi. don haka bacteria ta samu wajen zama
kenan. sai ya haifar masa
da kaikayin matse-matsi
da kaikayin gaba. MAGANI :
**********
hanyoyin magance
matsalar sun hada da:
1. Yin Wanka akan lokaci.
2. Tabbatar da cewa
matse-matsinka ya bushe
kafin ka sanya suturarka.
3. Ka dena sanya
Underwear ko wanduna matsattsu.
4. Ka nemi Anti Fungal
Creams ko Powder suna
nan a chemists ana
sayarwa.
5. Ka guji yin wanka da garin sabulu (detergents)
irin su Omo sauransu. anyi
su ne domin wanki ba wai
wanka ba. Kuma amfani
dasu zai rage ma fatar
jikinka Quality.
6. Ka samu ruwan danyen
zogale ka rika gogawa
awajen. shima zai yi maka
maganu sosai.
7. Man Habbah, Man
Zaitun, idan aka sanyasu akan fatsr wajen za’a samu
sauki sosai. Allah ya sawwake.
A kasa kuma Tambayoyi da amsa ne kan kaikan gaba da kuma kara karfin Mazakuta.
1.Matata ce take fama da kaikayin gaba ataimaka mana da Magani.
2. Maganin karfin mazakuta saboda shekaruna basuwuce talatinba amma idan ina jimai daga naje sau daya sai innakoma a Karo nabiyu sai gabana ya mutu. Ataimaka mana da magani nagode. Daga U. Abdullah.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu. Shi kaikayin gaba yana da dalilai da suke kawoshi. Idan ba’a magance ainahin dalilin ba, to gaskiya za’a dade ana shan magani amma ba za’a samu nasara sosai ba.
Idan tana da Jinnul Ashiq (Aljanin soyayya) wanda ke zuwa yana saduwa da ita, to lallai zatayi fama da Qaikayin gaba. Kuma ba ya jin magani har sai an magance ainahin aljanin dake tare da ita tukunna.
Idan kuma wata chuta ce wacce ake dauka ta hanyar Jima’i, to shima sai an maganceshi kafin Kaikayin ya dena.
– Ta nemi garin Hulba cokali 2, garin Magarya shi kuma cokali uku, garin lalle cokali biyu. Ta hadasu waje guda ta gauraya. Sannan ta rika diba tana dafawa tana zama cikin ruwan dumin.
Sannan ta nemi AL-MUMTAZ na Zauren Fiqhu ta rika yin matsi dashi. In sha Allahu zaku ga abin mamaki. Domin in sha Allahu kaikayin zai dena, kuma zata samu lafiya da ni’ima sosai.
2. Kai kuma ka nemi Man Jirjir ka rika zuba cokali guda acikin ruwan Lipton kana sha kullum bayan Sallar Isha’i. In sha Allahu zaka samu Qarfi sosai.
Amma ka hada da motsa jiki, da kuma kulawa da yana n abincin da kake ci.
WALLAHU A’ALAM.
Karin Shawara kan maganin Kaikan gaba
mallam da mafificin alkhairi bisa taimakon da kake wa al’ummar Annabi s.a.w game da abinda ya shige mana duhu na addini da ma na lafiyar mu. Mallam don Allah taimako nake nema, Mata ke fama da kaikayin gaba, a da ciwon Mara ke yawan damunta amma yanzu ya dena sai kaikayin gaban kuma tana complain cewa wannan yar fatar ta cikin farjin ta ke kaikayin, gashi kuma tana da ciki wata 5, amma mallam tun da nake da ita ban taba jin dadin saduwa da ita ba sai nazo yin inzali nake ji. Mallam ataimaka don naga ta fara shiga damuwa. Sannan kuma mallam ina bukatar shawarwi game da abubuwan da ya kamata in hada mata don karin lafiya gareta da jaririn dake cikinta. Nagode Allah Ya jikan mahaifa.
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullah wa barakatuh. Matsalar kaikayin gaba yawancin mata da yawa suna fama dashi, kuma yana da dalilai masu yawa da suke kawoshi.
MISALI KAMAR:
1. Rashin Tsaftace wajen ko askeshi akan kari.
2. Yawan yin tsarki da ruwan sanyi marar tsafta.
3. Sanya wando mai damshi.
4. Wanke gaba da sabulu.
5. Shan magunguna wadanda ba’a tabbatar da sahihancinsu ba.
7. Matsalar Shafar Aljanun Soyayya (JINNUL ASHIQ).
Yawancin lokaci irin wannan larurar tana da wuyar magani agun likitocin Zamani. Musamman ma idan Aljani ke kawota. Dole sai anyi maganin Aljanin, an kamashi a umurceshi ya dauke ajiyar da yayi awajen.
Amma dai koma menene musabbabin abun, ga wasu magunguna nan masu inganci a jarraba. in sha Allahu za’a dace:
1. APPLE VINEGAR (KHAAL TUFFAH) : Arika hadashi da ruwan dumi ko kuma hakanan yadda yake, ana chuda wajen, anan watsawa sosai.
2. INGANTACCEN GARIN HULBA : Arika dafawa cokali 3 ruwa kofi biyu, ahada da cokali biyar na Khal Tuffah ko farin Khal (White Vinegar). Idan ya dahu sannan a surka ruwan arika shiga ciki ana dumama wajen. Bayan nan a shafa Man Hulba ko Man Na’a-Na’a, ko Man habbatus sauda mai kyau. ko kuma a sanya turaren Farin Miski.
In sha Allahu za’a dace.
3. MUMTAZ : Wani magani ne wanda ZAUREN FIQHU ya hadashi musamman saboda mata wadanda sukayi haihuwa da yawa. Yana tsuke mace, kuma yana maganin kaikayi da kurarrajin gaba. Da kuma bushewa ko jin zafi yayin saduwa.
Idan an sameshi ana iya yin Matsi dashi sai bayan Awa guda ko awa biyu aje awankeshi da ruwan dumi. Za’a ci gaba dayi har tsawon sati uku.
In sha Allahu za’a samu waraka daga matsalar.
WALLAHU A’ALAM.
Wadannan shawarwari da magunguna an samosu ne daga Zauren Fiqhu, Shafin Ma’aurata.
Sannan a sani cewa magungunan gargajiyane. Idan bayan kwana 2 ba’a samu sauki ba to a garzaya Asibiti.Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole