Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata su yi lalle akwai sirrika acikin sa.
Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.
In kina son gyara fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki sha mamaki in sha Allah:
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun zakiga canji.
sannan gamai son kamshin fata:
Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.
Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk zakiga canjin fata in sha Allah.
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki: fata zatayi laushi, haske da kuma santsi.
Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki jika kamar botiki ba ruwa ruwa sosai ba Kamar dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki zakiga canji.
Daga karshe kuma ga masu fama da pimples, sai ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskaar ki, kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi. Kuma lalle dai ba bleaching yake ba.