Mafi yawancin mata sukan yi jinin al’ada na tsawon kwanaki 4 zuwa 7 ne.
Yawanci ana yin jinin al’ada ne bayan kwanaki 28. Sannan wasu matan sukan yi shi bayan kwanaki 21 ko 35 duk idan hakan ta faru ba matsala bane.
Jinin Haila yakan zama mai wasa ta hanyar canjawar kwayoyin halitta, shan wasu magunguna, shiga halin damuwa ko matsi, da dai sauran dalilai.
Zaki iya gane cewa jinin Al’adarki ya zama mai wasane idan wadannan abubuwan suka faru:
I dan jinin Al’ada yazo a kasa da kwanaki 21.
Ko kuma idan ya wuce kwanaki 35 bai zo ba.
Rashin ganin jinin al’ada sau 3 a jere.
Ganin Jinin Al’ada me kauri fiye da yanda aka saba gani ko ganin wanda ya tsinke sosai fiye da yanda aka saba gani.
Jinin al’ada wanda ya wuce kwanaki 7 ana yinsa.
Idan ya zama jinin Al’ada ya sassaba kwanakin da yake zuwa, misali yazo a kwanaki 28, sannan na gaba ya zo a kwanaki 38, sai kuma na gaba yazo a kwanaki 29.
Jinin al’adar dake zuwa da matsalolin amai, rawar jiki, zazzabi da zafi mai radadi.
Zubar da jini bayan gama jinin al’ada.
Idan ya zamana kina canja pads ko kunzugunki duk bayan awa.
canjin kwanakin jinin al’ada muddin bai kai na tsawon kwanaki masu yawa ba,ba matsala bane. Hakanan canjin kalar jinin shima muddin ba me yawa bane ba matsala bane.
Ciwukan dake kawo jinin Haila Mai Wasa:
Akwai cutar Amenorrhea: Mace zata iya gane da kamu da cutar Amenorrhea ne idan jinin al’adarta ya tsaya gaba daya ya daina zuwa.
Idan ya zamana jinin al’adar ki ya daina zuwa har tsawon kwanaki 90 kuma ba ciki gareki ba, ba shayarwa kike ba, sannan baki kai shekarun daina jini ba ko daina haihuwa(watau shekaru 45 zuwa 55) ba to akwai kyakkyawan zaton cutar Amenorrhea ta kamaki.
Hakanan karamar yarinya wadda bata fara jinin al’ada ba har ta haura shekaru 15 zuwa 16. Ko kuma bata fara jinin al’ada ba bayan shekaru 3 da fara fitowar nonuwanta to itama masana ilimin kimiyyar lafiya sunce ta kamu da cutar Amenorrhea.
Akwai kuma cutar Oligomenorrhea: Ita wannan cuta ana ganeta ne idan mace tana zarta kwanakin da aka saba ganin jinin al’ada a cikinsu,watau tana kai kwanaki 35 kamin yin jinin. Ko tana yin jinin sau 6 zuwa 8 a shekara.
Akwai kuma cutar da ake cewa Dysmenorrhea: Mace zata iya gane ta kamu da cutar Dysmenorrhea ne idan tana jin zafi me tsanani a yayin jinin al’adarta. Jin zafi wanda ba mai tsanani ba bashi da illa.
Zubar da jini bayan kammala jinin al’ada shima matsalace wadda alamace ta rashin lafiya.
Abubuwan dake kawo Jinin Haila Mai Wasa:
Abubuwan dake kawo jinin Haila mai wasa sun hada da fitowar wani abu da ake cewa Endometriosis a gaban mace. Wannan abu idan ya fito ba daidai ba yana haddasa illa ga mata.
Akwai kuma cutar PID: Ita wannan cuta tana kama kasusuwan gaban mace ne wanda kuma silarsu itace cutar da ake dauka ta wajan jima’i da aka bari ta dade ba’a yi maganinta ba.
Hakan yakan kawo ciwon mara sosai, da fitar da ruwa a gaban mace mai wari da kuma rikicewar jinin al’ada.
Hakanan akwai abinda ake kira da (PCOS): shima wannan yakan sa jikinki ya fitar da wasu kwayaye wanda ke hana Ovulation ko ya jinkirtashi.
Hakan yakan kawo jinin Haila Mai Wasa ko ya dakatar da jinin hailar gaba daya.
Zubar da jini sosai lokacin al’ada shima alamar cutar ne.
Akwai wasu kalar cutar daji watau Cancer dake taba yanayin jinin al’adar mace.
Karin kiba ko rama me yawa na iya yin illa ga yanayin jinin hailarki.
Motsa jiki fiye da kima wanda kesa a samu karancin Fat a jikin mace na iya taba yanayin jinin al’adarta.
Shan Maganin Hana Haihuwa: Shan Maganin Hana Haihuwa na iya dakatar da jinin haila na tsawon watanni 6.
Yin bari ko zubewar ciki ma na iya kawo matsalar jinin Haila me wasa.
Hanyoyin kaucewa kamuwa da matsalar jinin haila me wasa
A rika motsa jiki a hankali ba sosai ba wanda zai iya zama illa, kada ayi canjin abinci ko shan magani wanda zai zubarwa mace da jiki sosai yasa ta rame lokaci daya.
A rika samun hutu sosai.
A rika amfani da maganin hana haihuwa kamar yanda likita yace.
A rika canja Pads ko Kunzugu duk bayan awanni 4 ko shida dan kaucewa kamuwa da cuta.