Babu wata hanya da ake amfani da ita wajan dawo da budurci da zaran mace ta rasashi.
Saidai a al’adance ana bayar da magungunan matsi wanda ake ikirarin suka sa gaban mace ya matse bayan ta rasa budircinta.
Rasa budurci ba yana nufin gaban mace zai bude bane, hakanan ba dole mace sai ta ga jini ba bayan rasa budurcinta ba.
A likitance ma akan yiwa mace aiki ta yanda gabanta zai tsuke idan ya kasance ya bude da yawa. Abubuwan dake sa gaban mace ya bude sun hada da haihuwa da yawan shekaru.