Thursday, December 26
Shadow

Hotuna Gwanin ban Tausai na wata likita bayan masu Gàrkùwà da mutane sun sakota

Wata likita me suna Dr. Ganiyat Popoola da dan uwanta sun shafe watanni 10 a hannun masu garkuwa da mutane a Kaduna amma yanzu ta samu kubuta.

Hotunansu da aka gani bayan sakosu daga hannun masu garkuwa da mutanen musamman idan aka yi la’akari da hotunansu na kamin a kamasu ya baiwa mutane mamaki da tausai sosai.

Matar dai tana aiki ne a asibitin ido na National eye Center dake Kaduna kuma tun ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2023 aka yi garkuwa da ita da mijinta, Nurudeen Popoola, da kuma dan uwanta, Folaranmi Abdul-Mugniy.

Bayan tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da su, sun sako mijin amma suka ci gaba da rike matar, da dan uwanta, Abdul-Mugniy.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: 'Yansanda sun kama 'yan kasar China 80 suna ayyukan damfarar yanar gizo a Abuja

Ranar 30 ga watan October ne dai shugaban kungiyar likitoci ta Resident Doctors, Tope Osundara ya tabbatar da kubutar matar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *