Monday, December 16
Shadow

Wata Sabuwa: Kananan yaran da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu bisa zargin cin amanar kasa na iya fuskantar hukuncin kìsà

Rahotanni sun bayyana cewa hukuncin kisa na daga cikin hukuncin da kananan yara da gwamnatin tarayya ta gabatar a kotu a Abuja zasu iya fuskanta.

Yaran dake da shekaru 14 zuwa 17 su 29 ko 32 a wasu rahotannin sun baiwa mutane tausa yi sosai bayan ganinsu cikin tashin hankali,yunwa da rashin lafiya.

Yaran sun rika yanke jiki suna faduwa saboda yunwa bayan da aka gabatar dasu a kotu, saidai Hukumar ‘yansandan Najeriya tace duk karya suke kawai dan su jawo cece-kuce ne.

Saidai duk wanda ya ga yaran yasan suna cikin tashin hankali dan idanuwansu sun yi zuru-zuru ga kasusuwan hakarkarinsu duk a waje ga jikinsu ba alamar kuzari duk dai alamun yunwa sun bayyana a tattare dasu.

Karanta Wannan  Rundunar 'Yan Sanda Ta Fitar Da Hotunan Jami'anta Guda Biyu Da Suka Mùțù A Yayin Aranģamar Su Da Yan Shi'a A Abuja A Makon Da Ya Gabata

Rahoton VOA yace yaran zasu iya fuskantar hukuncin kisa saboda shine hukuncin laifin cin amanar kasa da ake zarginsu dashi.

An saka dokar hukuncin kisa akan masu cin amanar kasa tun a shekarar 1970s amma tun shekarar 2016 ba’a ga wanda akawa hukunci da dokar ba.

Lauya me zaman kansa wanda yana daga cikin masu kare yaran daga zargin da gwamnati ke musu, Akintayo Balogun ya bayyana cewa, lamarin kai yaran kotu ya sabawa doka.

Yace sai yaro ya kai shekaru 19 ne sannan za’a iya kaishi kotu a tuhumeshi da zargin da akewa yaran.

Saidai idan zaku iya tunawa, hutudole ya kawo muku rahoton kakakin ‘yansandan Najeriya yana cewa da zarar yaro ya haura shekaru 7 za’a iya gurfanar dashi a gaban kotu.

Karanta Wannan  Hotuna: Wakilan hukumar zaben Najeriya, INEC sun ze saka ido a zaben kasar Amurka

Zuwa yanzu dai yaran suna can a gidan yari an tsaresu inda aka bayar da belinsu akan Naira Miliyan 10 kowannensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *